Tinubu Na Shirin Bin Tsarin Da Buhari Ya Bi Wajen Bayyana Ministocinsa, Bayanai Sun FitoJam’iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu na kan tattaunawa dangane sunayen ministocinsa da zai nada.

Shugaban jam’iyyar ta APC, Abdullahi Adamu ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin jam’iyyar na jihohi a Abuja a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.


Abdullahi Adamu ya ce a yanzu haka Tinubu na kan tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar dangane da mutanen da yake so ya bai wa mukaman ministocin.

Adamu ya kara da cewa da zarar ya kammala tattara sunayen wadanda zai nada, za a aika da su zuwa majalisa domin an tantance su kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Ya ce za a ji sunansu da zarar Tinubu ya mika su zuwa majalisa, inda daga bisani kuma za a rantsar da su bayan tantancewar.

Tinubu zai bayyana ma’aikatar da aka tura kowane bayan tantancewa

Abdullahi Adamu ya kuma kara da cewa Tinubu zai tura da sunayen ne kawai ba tare da bayyana ma’aikatar da zai ba kowanensu ba.

Ya ce sai bayan majalisa ta tantance su ne zai bayyanawa ‘yan kasa inda ya tura kowane daga cikinsu kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa.

Wannan wani tsari ne da tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zo da shi a shekarar 2015 lokacin da yake shirin nada ministocinsa.

A bisa doka, dole ne shugaban kasa ya bayyana ministocinsa da sauran mambobin majalisarsa a cikin kwanaki 60 na farko a ofis.

Saboda haka, shugaba Tinubu na da har zuwa ranar 28 ga watan Yuli kafin bayyana ministocinsa tare da mika sunayensu ga majalisa domin tantance su.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN