Daga Ƙarshe, An Bayyana Yawan Ministocin da Shugaba Tinubu Zai Naɗa Nan da Kwanaki Kaɗan



Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai naɗa ministoci 36 zuwa 42 a gwamnatinsa. Legit ya wallafa.

Daily Trust ta tattaro cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tilasta wa shugaban ƙasa ya naɗa minista ɗaya daga kowace jiha a Najeriya da kuma ƙarin minista ɗaya daga kowace shiyya.

Idan zaku iya tuna wa, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa ministoci 36 a zangon mulkinsa na farko, amma a zango na biyu ya ƙara suka kai 42.

Adadin ministoci nawa shugaba Tinubu zai naɗa a halin yanzu?

Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na kafar watsa labaran Channels tv, Sanata Omisore ya ce yawan Ministocin da Tinubu zai naɗa na tsakanin 36 zuwa 42.

"Kundin tsarin mulki ya ce minista ɗaya daga kowace jiha jimulla 36 kenan da kuma minista ɗaya daga kowace shiyya, idan muka haɗa ya zama 42, wuƙa da nama na hannun shugaban ƙasa."

"Saboda haka ko dai ya naɗa ministoci mafi ƙaranci 36 ko kuma mafi yawa 42," inji Sakataren APC na ƙasa, Omisore.

"Har yanzun muna kan aikin neman shawarin jam'iyya, muna kokarin tsara jerin ministocin. Muna fatan haɗa tawagar ministocin da zata yi daidai da bukatar 'yan Najeriya."

Yayin da aka tambaye shi ko shugaba Tinubu na tunanin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa tare da mambobin jam'iyun adawa kamar Nyesom Wike, Omisore ya ce wuƙa da nama na hannun shugaban ƙasa.

Ya ce a halin yanzun shugaban kasa na ci gaba da tattaunawa da jam'iyya mai mulki dangane da sunayen ministocin da zai naɗa, kamar yadda Dailypost ta ruwaito.

Shugaba Bola Tinubu Na Daf Da Bayyana Sunan Sabon Wanda Ya Nada Mukami

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku rahoton cewa Shugaba Bola Tinubu yana shirin sanar da sabon wanda ya nada mukami kowanne lokaci daga yanzu.

Ana sa ran nan ba da dadewa ba Shugaban Kasar zai sanar da Hakeem Muri-Okunola, shugaban ma'aikatan jihar Legas , a matsayin babban kebabban sakatarensa.

Published by isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN