Shugaba Tinubu Ya Yi Ƙus-Ƙus da Sabon Shugaban EFCC a Villa, Bayanai Sun Fito


Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da sabon muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC). Legit Hausa ya wallafa.

Tinubu ya gana da sabon muƙaddashin shugaban EFCC, Abdulkarim Chukkol, a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba, 12 ga watan Yuli.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkoki kafafen sada zumunta na zamani, D. Olusegun ne ya tabbatar da haka a shafinsa na tuwita.

Ya rubuta a shafinsa cewa:

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin muƙaddashin shugaban hukumar EFCC, Mista Abdulkarim Chukkol a fadarsa."

Wannan ganawa ta ranar Laraba na zuwa ne makonni hudu bayan Tinubu ya dakatar da Abdulrasheed Bawa daga matsayin shugaban EFCC har sai baba ta gani daga ranar 14 ga watan Yuni, 2023.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN