Sufeton yan sanda ya saci jariri, runduna ta kore shi daga aiki


Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta amince da korar Sufeto Samuel Ukpabio.

 An sallami jami'in saboda zargin satar jarirai.

 Da yake sanar da korar jami’in a wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Twitter da aka tabbatar, mai magana da yawun rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya bayyana cewa an amince da korar jami’in ne a ranar Alhamis domin share fagen gurfanar da shi.

 Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Idowu Owohunwa, ya sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da ka'idar aiki ga ‘yan sandan Legas bisa doka, wayewa da mutunta ran dan Adam.

 Ku tuna cewa wata mata ‘yar shekara 35 mai suna Fortune Ohafuoso, ta zargi Ukpabio, wanda ke aiki a Panti Division, da hada baki da wasu don sace jaririnta.

 Mahaifiyar mai yara uku ta bayyana cewa Ukpabio ya kama ta kuma ya zarge ta da yunkurin siyar da jaririyar a kan N3m kuma ya tilasta mata ta rubuta bayani a kan hakan.

 Obhfuoso ya yi ikirarin cewa Ukpabio da karfin tsiya ya kwace sabon jaririn da ta haifa tare da ba wata mata da ba a tantance ba kwana daya bayan ta haihu.

 Ta ce Ukpabio ya ba ta Naira 185,000 kuma ya yi mata barazanar cewa ba za ya sake dawowa da yaron ba ko kuma ya kama ta ya kwace mata sauran yaran biyu.

 Daga karshe ta kai rahoton faruwar lamarin ga wani mai fafutukar kare hakkin jama’a, Dokta Abiola Akiyode-Afolabi, wanda ya roki jami’an tsaro da su shiga cikin lamarin.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN