Mata da yara na daga cikin wadanda abin ya shafa, kamar yadda shaidun gani da ido suka shaida wa BBC.
An kai harin ta sama a yankin Dar es Salaam na Omdurman, daura da gabar kogin Nilu zuwa babban birnin kasar Khartoum, a safiyar ranar Asabar.
Tun a watan Afrilu ne dai sojoji da dakarun sa-kai suke fafatawa don kwace babban birnin kasar.
Rikicin dai ya faro ne bayan da shugaban rundunar sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma shugaban rundunar sojojin gaggawa ta RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo suka yi takun-saka kan makomar kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani jami’in kiwon lafiya na jihar Khartoum ya ce akalla mutane 22 ne suka mutu a harin na ranar Asabar, yayin da RSF ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 31.
Published by isyaku.com