Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya bayyana cewa yayin da wasu ma’aikatansa ke da gidaje a kasashen waje da suke amfani da su a matsayin gidajen hutu, ba shi da ko daya.
Dan kasuwan ya kara ba da wasu shawarwari don samun nasara a matsayin mutum a fagen kasuwanci. Daily trust ta rahoto.
A wata hira da Business Insider Africa da aka buga kwanan nan a shafin yanar gizon Tonyelumelufoundation na Instagram da aka tabbatar, Dangote ya ce, “Mutane da yawa har da kanana, ya kamata mu yi taka tsantsan saboda mukan wuce wuri har da farwa uwar jarinmu mu ’yan Afirka, shi ne muke kashe kuÉ—in da aka yi hasashe bisa tsari.
“Da zarar ka fara kasuwanci kuma sana’ar ta fara kyau, maimakon ka ci gaba da saka hannun jari a cikin sana’ar, sai ka fara kashe kudi kana tunanin za a ci gaba da samun riba. Akwai abubuwa da yawa a cikin kasuwanci don haka kuna buÆ™atar mayar da hankali sosai."
Dan kasuwar ya ci gaba da ba da shawarar cewa samun kayan alatu na iya zama dagula hankali.
Da yake ba da misali da kansa, Dangote ya bayyana cewa, “Abubuwan alatu - suma daukar lokacinku wanda ba zai sa ku mai da hankali kan kasuwancin ku ba. Ina nufin, ba ni da wani gidan hutu a ko'ina; Ba ni da gida a ko'ina amma na san mutanen da suke yi mini aiki, suna da gida a Landan. Amma ba ni da."
Published by isyaku.com