Ma’aikatan MRS Oil Nigeria Plc guda takwas da aka yi garkuwa da su a makon jiya a Legas sun samu ‘yanci, inji jaridar The Nation.
An sako mutanen ne a daren Lahadi a unguwar Sangotedo da ke jihar Legas.
Sai dai babu tabbas ko an biya kudin fansa don 'yancinsu.
An sace ma’aikatan man ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin yayin da suke cikin wani jirgin ruwa mai zaman kansa daga tsibirin Legas zuwa Lekki.
An ce wadanda suka yi garkuwa da su sun shiga cikin kwale-kwalen da suke ciki, inda suka sace su suka bar kwale-kwalen ma’aikatan mai da kayansu a ciki.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa jaridar The Nation sako ma’aikatan mai a safiyar ranar Litinin.
Da aka tambaye shi ko an kama wadanda suka sace mutanen, Hundeyin ya mayar da martani da kakkausan harshe, inda ya ki karin bayani kan lamarin.
Published by isyaku.com