Bazawara ta kashe Yar sanda da yaranta biyu ta banka wa gawarsu wuta


Rahotanni sun bayyana cewa wata bazawara mai suna Nneamaka Nwosu, ta jefa al’ummar Nnokwa, da ke karamar hukumar Idemili ta kudu a jihar Anambra cikin jimami bayan ta kona wata ‘yar sanda da ‘ya’yanta guda biyu.

 Matar ‘yan sandan da ta mutu, ta taimaka wa Nwosu ne da masauki a gidanta bayan mijinta ya sake ta, ta zama marar gida kuma tana matukar bukatar masauki.

 An ce ‘yar asalin garin Amawbia ce a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.

 Da yake ba da labarin abubuwan da ya kai ga kisar Yar sanda da yaranta biyu, wani mazaunin unguwar ya ce, “Da mijin ya sake ta, ta gaya wa ‘yar sandan da ta ba ta masauki a gidanta.

 “A wannan rana mai muni, ta yi rigima da ’yar sandan da ya kai ga fada.  Ta bugi ‘yar sandan da Tabarya a kai ta fadi ta sume.

 “Da sauri ta daure ‘yar sandan da ‘ya’yanta guda biyu da igiya a cikin dakinsu sannan ta banka musu wuta tare da ginin,” in ji shi.

 An tattaro cewa, ‘yan banga na yankin da kuma wasu mutanen kauyen da gobarar ta ja hankalinsu ne suka kama wadda ake zargin, a lokacin da take kokarin tserewa.

 Lokacin da dan bangan ya yi mata tambayoyi, tun farko ta musanta aikata laifin, inda ta ce lamarin fashewar iskar gas ne yayin da marigayiyar da ‘ya’yanta ke tafashen ruwa.

 Daga baya Nwosu ta amsa laifinta, inda ta danganta laufin da aikin shaidan.

Ta ce “Ban san abin da ya same ni ba wanda ya sa na aikata laifin.  Na cancanci a harbe ni saboda wannan mugun aiki da yi wa wanda ta taimake ni a lokacinn da nike cikin bukata,” inji ta.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce an kama wanda ake zargin tare da ajiye gawar ‘yar sanda da ‘ya’yanta a dakin ajiyar gawa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN