Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wata mata mai suna Maimunatu Sulaiman ‘yar shekara 21 da haihuwa da laifin kashe mijinta da wuka a unguwar Kofar Dumi da ke jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Aminu Gimba Ahmed, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuli, 2023, ya ce wanda ake zargin ta daba wa mijinta Aliyu Mohammad wuka a kirjinsa bayan wata hatsaniya ta barke a tsakaninsu.
PPRO ya ce lamarin ya faru ne a gidan ma’auratan a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli, 2023, inda ya kara da cewa wacce ake zargin ta samu kananan raunuka a cikinta a lokacin fadan, ta amsa aikata laifin.
Published by isyaku.com