Wasu fusatattun jama’a sun kai hari kan wasu mutane biyu da ake zargin barayin babura ne, inda suka yi masu ruwan duwatsu a jihar Benue.
An tattaro cewa an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke kokarin kwace babura daga hannun masu su a Gyado villa da ke Makurdi a yammacin ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, 2023.
Har yanzu babu cikakken bayani kan lamarin har zuwa lokacin da ake gabatar da wannan rahoto, sai dai wasu mazauna birnin da suka wallafa hotunan, sun yi kira ga ‘yan sanda da su kubutar da wanda ake zargin daga hannun mutanen da suka fusata.
Published by isyaku.com