Wasu matasa sun kashe wata Dorina da suka ce tana addabar al'ummar gabar ruwa a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, 2023, kusa da Ebete, wani kauye da ke kan iyakar jihar Benue da Nasarawa.
Olikita Ekani, tsohon mai taimaka wa tsohon gwamnan jihar Benue kan harkokin yada labarai, Samuel Ortom, ya raba bidiyon yadda matasan suka kashe dabbar.
"Matasan Agatu sun kashe wani dodo da ke addabar magudanar ruwa a tsakanin Adeke da Ebete," in ji shi a bidiyon.
“A cewar daya daga cikin shaidun gani da ido, dabbar ta hana yawancin masunta gudanar da sana’arsu cikin walwala, ya tilasta su zama a cikin gida, tare da raunata wasu masunta.”
“Ya kuma kara da cewa ita dabbar ta cinye amfanin gona da lalata filayen noma a kauyukan da ke bakin kogi a Agatu.
"An yi zargin cewa dabbar ta kuma kashe wani mutum a Makurdi kusa da tsohuwar gada kafin ta tsere zuwa Agatu ta kogin Benue."
Published by isyaku.com