Majalisar wakilai ta ki amincewa da shirin kara kudin wutar lantarki


Hakan na zuwa ne bayan da Honourable Aliyu Madaki ya gabatar da kudirin nuna rashin amincewa da karin farashin, musamman idan aka yi la'akari da karin farashin man fetur da tuni ya yiwa 'yan Najeriya da dama illar tattalin arziki. Shafin labarai na isyaku.com ya samo


 Dan majalisar ya ce bai dace ba a gabatar da irin wannan gagarumin karin kudin fito a daidai lokacin da 'yan kasar ke ci gaba da kokawa kan tasirin hauhawar farashin man fetur.


 Bayan amincewa da kudirin, majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da harkokin mulki, da zarar an kafa shi, ya shiga tattaunawa da NERC.  Manufar ita ce neman fahimtar juna don tunkarar shirin karin kudin fito, la'akari da kalubalen tattalin arziki da jama'a ke fuskanta a halin yanzu.


 'Yan majalisar sun jaddada aniyarsu ta kare muradun 'yan Najeriya tare da tabbatar da cewa hukunce-hukuncen da hukumomi suka yanke sun dace da jin dadin 'yan Najeriya.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN