A kalla 'yan ta'adda 22 ne sojojin saman Najeriya suka kashe a kananan hukumomin Batsari da Jibia a jihar Katsina. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta yi nasarar kashe ‘yan ta’addan, galibin ‘yan ta’addan yaran kasrgumin Dan ta'adda Abdulkareen Lawal ne, wanda aka fi sani da Abdulkareen Boss, a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.
An kashe dan ta’addan tare da wasu dakarunsa a wani hari ta sama a dajin Ruga da ke Katsina a ranar 5 ga Agusta, 2022. An zarge shi da kitsa kisan wani kwamandan ‘yan sandan Najeriya a Dutsin Ma a ranar 5 ga Yuli, 2022.
An bayyana a ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli cewa harin da sojojin saman Najeriya suka kai ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan ta’addar bisa bayanan sirri da sojoji suka samu.
Majiyar sojan ta ce, “Sama da ‘yan ta’adda 22 akasarinsu dakaru ne na sarkin ‘yan ta’addan marigayi Abdulkareen Lawal, wanda aka fi sani da Abdulkareen Boss, a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023, an kashe su a wani hari ta sama da rundunar sojin saman Operation Hadarin daji ta kai a Batsari da Sola Poi II a kananan hukumomin Batsari da Jibia a jihar Katsina.
“An kai harin ne biyo bayan samun rahotannin sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addan ne ke da alhakin sace-sacen mutane da kuma munanan hare-hare a wasu al’ummomi a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.”
Kakakin NAF, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da harin ta sama da aka kai kwanan nan a ranar Litinin.
Published by isyaku.com