Maigida da kaninsa sun yi wa kwarto dukan ajali bayan ya kama shi turmi-tabarya tare da matarsa


An kama Tukur Sale da kaninsa Ibrahim Sale bisa zargin kashe wani magidanci bisa zargin yin lalata da matarsa.


 Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, ‘yan uwan ​​biyu da suka fito daga kauyen Ngurore -Chigari a karamar hukumar Fufore a jihar Adamawa, an yi zargin cewa sun yi wa Usman Sale duka da adda da sanduna har lahira, bayan da aka ce an kama shi turmi tabarya da matar Tukur.


 An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban wata babbar kotun majistare da ke Yola.


 Dan sanda mai shigar da kara, Insifekta Zakka Musa, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun kai wa marigayin hari da adda da sanduna a ranar 30 ga watan Yunin 2023, wanda ya yi sanadin rasuwarsa.


 A cewarsa, an garzaya da mamacin zuwa Asibitin Cottage dake garin Fufore inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.  Ya ce laifin ya sabawa sashe na 60 da 141 na dokar penal code.


 Sai dai Tukur ya dora laifin abin da ya aikata a kan tsokanar ban haushi.


 "Na sha gargadin shi sau da dama ya daina fita da matata, amma ya ki," in ji Tukur.


 “Na bi shi ne bayan na gan shi tare da matata, shi ne ya fara buge ni da sanda, kanena Ibrahim ya zo ya cece ni.” Ya kara da cewa.


 Alkalin kotun, Alheri Ishaku ta bayar da umarnin tsare mutanen biyu tare da dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Yuli, 2023, bayan wadanda ake kara sun amince da aikata laifin.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN