Wani direban mota ya kashe wani mataimakin Supritanda ‘yan sanda (ASP) da ke aiki a rundunar ‘yan sandan jihar Ondo.
An murkushe jami’in ne har lahira a wani shingen binciken ababen hawa da ke kan titin Benin-owo da ke Ifon a cikin karamar hukumar Ose ta jihar a ranar Lahadi, 23 ga Yuli, 2023.
A cewar shaidun gani da ido, jami’in da ya rasu ya yi kokarin tsayar da motar amma direban ya buge shi ya tafi ba tare da ya tsaya ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Misis Funmilayo Odunlami, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce sojojin Najeriya sun kama direban a Sobe a jihar Edo.
Hukumar ta PPRO ta musanta rahoton da ake jita-jita a baya cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe dan sandan a kan hanyar. Ta ce buge Jami'in aka yi da mota aka gudu.
“Wata mota da ake zargi, yayin da ‘yan sanda ke kokarin tsayar da direban, bai tsaya ba. Don haka, an sanar da jami’an mu a kan babbar hanya amma da isa wani wuri da ke kusa da Ifon, direban ya karkata ya bugi ASP kuma jami’in ya mutu nan take.” Inji Odunlami.
"Duk da haka, an bi direban, kuma mun yi sa'a shi (direba) sojoji sun kama shi a Sobe a jihar Edo."
Kakakin ya kara da cewa an ajiye gawar dan sandan da ya mutu a dakin ajiyar gawa.
Published by isyaku.com