Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a bayyana yadda aka kashe kimanin dalar Amurka biliyan 5 da Abacha ya wawushe da gwamnatocin tsoffin shugabannin kasar Olusegun Obasanjo, Umaru Musa Yar’Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari suka kwato.
Kotu ta umurci gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta bayyana ainihin adadin kudaden da Janar Sani Abacha ya wawure daga Najeriya, da jimillar kudaden da Abacha ya kwato da duk wata yarjejeniyoyin da gwamnatocin tsoffin shugabanni Obasanjo, da ‘Yar’adua suka sanya wa hannu a kai har da Jonathan da Buhari.”
Daily trust ta rahoto Mai shari’a James Kolawole Omotosho ne ya yanke hukuncin a makon da ya gabata, biyo bayan wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/407/2020, wadda kungiyar kare hakkin zamantakewa da tattalin arziki (SERAP) ta kawo.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Omotosho ya ce, “A karshe, bukatar da SERAP ta gabatar ya dace kuma gwamnatin tarayya ta ma’aikatar kudi ta bayar da umarnin mika wa SERAP cikakken bayanin kashe kimanin dala biliyan 5 da Abacha ya sace cikin kwanaki 7. akan wannan hukuncin."
Published by isyaku.com