Wasu gungun matasa a yankin Ubeji da ke karamar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, karkashin kungiyar matasan Ubeji Youth and Employment Development Organisation, sun yi kakkausar suka ga ‘yan matan da ke sanya suturar da ba ta dace ba.
A cewar jaridar Punch, mambobin kungiyar matasan sun fara danne wadanda ake zargi da aikata laifin ta hanyar yi musu bulala ko kuma a madadin sanya musu tara.
An tattaro cewa aiwatar da atisayen mai lakabin ‘Yaki da sanya tufafin da ba su dace ba’ a tsakanin matasa mata a cikin al’umma, wanda ya fara tun ranar Litinin, 3 ga watan Yuli, 2023, ya haifar da firgici a tsakanin mata a yankin.
Wasu daga cikin wadanda abin ya shafa, an ce an tilasta musu su biya tarar da ta kai Naira 10,000 ko kuma a yi musu bulala 40 da sanda.
Sakataren kungiyar matasa Stanley Bomele, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaidawa manema labarai cewa " atisayen ya zama dole saboda yadda mata suke sanya tufafi a cikin al'umma."
Ya kara da cewa, "Yawancin 'yan matan suna amfani da sunan saye-saye ne da sunan kwalliya inda wasunsu suka kusa yin tsiraici, abin da ke da ban haushi kuma ba ya yiwa al'umma dadi."
Bomele ya danganta babban dalilin cin zarafin mata a yankin da sanya tufafin da bai dace ba ne a tsakanin 'yan mata.
"Ba za a ƙara amincewa da saka riguna, guntun wando ko matsattsun wando ba daga Yan mata a cikin al'umma," in ji shi.
Published by isyaku.com