Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa kwamitin bincike da zai binciki duk wani rabon fili da kadarorin gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjonsa a zamanin Gwamna Aminu Tambuwal.
Kwamitin mai mutum 5 ya kasance karkashin jagorancin mai shari’a M.A. Pindiga (rtd) yayin da Barista Nasiru Muhammed Binji zai kasance sakataren kwamitin. Jaridar Daily trust ta rahoto.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Cif Jacob E. Ochidi, SAN; Alhaji Usman Abubakar da Barista Lema Sambo Wali.
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamna Ahmed Aliyu ta bayyana cewa, kwamitin zai kuma tantance asusun bankin gwamnati da adadin da aka samu daga tallace-tallace da kuma gwanjon kadarorin.
Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai yi nazari kan yadda aka raba filaye daban-daban a duk fadin jaha ciki har da gidajen gwamnati da aka sayar ko aka yi gwanjo.
An baiwa kwamitin watanni biyu daga ranar zamansa na farko da ya gabatar da rahotonsa.
Published by isyaku.com