Hukumar DSS ta tsare tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari


Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma, Abdulaziz Yari. PM News ta rahoto.

 A halin yanzu jami’an DSS ne ke gasa Yari.

 Har yanzu dai ba a bayyana dalilin tsare shi da kuma yi masa tambayoyi ba.

 SUNDAY PUNCH  ta ruwaito wata majiya kusa da dan majalisar tana cewa Yari ya kai rahoto a ofishin ‘yan sandan sirri bayan kammala zaman majalisar a ranar Alhamis.

 Rahotanni sun bayyana cewa majiyar ta yi ikirarin cewa ta raka dan majalisar zuwa ofishin DSS domin amsa gayyatar da aka yi masa.

 “Sanata Yari har yanzu yana hannun DSS, amma sai ya fita nan ba da jimawa ba in sha Allahu.  Bayan kammala taron yaje ofishin su da kanshi.  Na yi masa rakiya, kuma yana can tun a wancan lokacin,” in ji majiyar PUNCH.

 Sai dai bai bayyana dalilin da yasa hukumar tsaro ta gayyaci dan majalisar ba.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN