Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tsohon shugaban APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatare, Iyiola Omisore a fadarsa Aso Rock. Legit ya wallafa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wannan gana wa na zuwa ne mako ɗaya bayan Adamu da Omisore sun yi murabus daga kan muƙamansu.
Abdullahi Adamu da Omisore sun sauka daga kujerun shugaban APC da Sakatare awanni kaÉ—an gabanin ranar taron shugabanni da taron majalisar zartarwa (NEC).
A lokacin shugaba Tinubu yana Kenya inda ya halarci taron ƙungiyar tarayyar Afirka kuma tunda ya dawo bai zauna da tsoffin shugabannin ba sai yau Talata, 25 ga watan Yuli.
Haka nan kuma Adamu, tsohon gwamnan Nasarawa ya ƙi yarda ya ce komai kan abinda ke faruwa a APC, ya ce a jira sai Bola Tinubu ya dawo Najeriya.
Duk da ba bu bayani a hukumance kan abinda zasu tattaun, ana hasashen wanna gana wa zata maida hankali ne kan batutuwan da shuka shafi abinda ke wakana kan shugabancin APC.
Published by isyaku.com