Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garin Karim da kewaye sakamakon hare-haren da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kaddamar a wasu kauyukan karamar hukumar Karim Lamido.
Sakataren yada labarai na gwamnan, Yusuf Sanda, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce dokar hana fita ta biyo bayan sabon rikicin kabilanci a wasu sassan karamar hukumar Karim Lamido na jihar.
Ya ce an wajabta wa jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda, kuma duk wani mutum ko gungun mutanen da aka samu sun karya wannan doka za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar ta umurci dukkan masu unguwanni, sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Karim Lamido da su lura da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya.
Published by isyaku.com