An tsinci jariri a raye a bayan mahaifiyarsa sa'o'i 24 bayan 'yan bindiga sun harbe ta

 

An gano wani yaro dan wata bakwai mai suna Habibu yana barci a bayan mahaifiyarsa sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga sun harbe ta a hanyar Pandogari zuwa Allawa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja. Daily trust ta rahoto.

 City & Crime ta tattaro cewa ‘yan bindiga sun tare hanyar Pandogari zuwa Allawa rana guda kafin Sallah, inda suka harbe fasinjoji shida, ciki har da wata dalibar SS 2 na Kwalejin Kimiyyar Mata ta Maryam Babangida, Minna, Hauwa Aliyu, da mahaifiyar jaririn har lahira.

 Shugaban kungiyar matasan Lakpma, Jibril Allawa, ya shaidawa City & Crime cewa, 

“Abin mamaki, jaririn na daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin da aka kashe mutane shida.  ‘Yan banga da suka je washegarin kwashe gawarwakin wadanda abin ya shafa sun gano jaririn yana barci a bayan mahaifiyarsa da ta mutu.”

 Ya bayyana cewa, “Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Yuni, kuma mutane shida sun rasa rayukansu.  Maryam ta kira ta sanar mana za ta zo gida don yin Sallah.  Muka ce mata ta koma makaranta ta yi bikin Sallah a can amma ta dage cewa tana son ta zo gida mu yi biki.

 “Wani Abubakar Ismail, dan shekara 16, wanda ya samu raunin harbin bindiga a kirjin sa, ya yi ta gudu kafin a ceto shi kuma yanzu haka yana samun kulawa a asibiti.”

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN