An firgita yayin da ake zargin sojoji sun kashe ‘dan banga da wata mata


Firgici ya mamaye al’ummar garin Eke da ke karamar hukumar Udi a jihar Enugu sakamakon zargin kashe wani dan sa kai na unguwar (‘dan banga) da wata mata da wasu sojoji na runduna ta 82 na rundunar sojojin Najeriya ta Enugu suka yi. The Nation ta rahoton

 An tattara ’yan banga Ebuka Oke (marigayi);  Mataimakin babban jami’in tsaro na Eke Security Neighborhood Vigilante Watch, Mista Emeka Anigbo;  Chinedu Okolo da Obinna Ofor suna kan hanyar su ne domin yakar ‘yan fashin da suka tare babbar hanyar cocin Katolika (Ugwudinso) da kuma Eke, kusa da kamfanin Ama Breweries a yammacin ranar Alhamis lokacin da sojojin suka nemi da su tsaya sai kuma suka fara harbi.

 An bayyana cewa yayin da aka harbe Ebuka Oke a wajen, harsashi ya fasa al'aurar Okolo da kafafunsa sakamakon harbin da sojoji suka yi masa tare da harbin Ofor a sassa daban-daban na jikinsa.

 Lamarin da ya jefa al’umma da makwaftan su cikin firgici.

 Daya daga cikin jami’an, Anigbo ya shaida wa manema labarai a kan gadon asibitinsa cewa: 

“Mun kasance a 9th Mile Conner a daren ranar Alhamis inda muka je bikin karrama abokan aikinmu da aka kaddamar a matsayin ‘yan sa ido a unguwanni.  A nan ne muka samu kira na gaggawa cewa ‘yan fashi da makami sun tare babbar hanyar da ta kai ga fitacciyar cocin Katolika (Ugwudinso) da Eke, kusa da gidajen sayar da giya na Ama.

 “Lokacin da muka samu kiran, mun yi watsi da abinci da abubuwan sha da muke shirin ci, kuma cikin gaggawa muka fita da nufin fuskantar ’yan ta’adda, amma saboda cunkoson ababen hawa da suka samu sakamakon toshewar hanyar, ba mu iya zuwa wajen da motarmu ba."

 Ya kara da cewa sun yanke shawarar tsayar da motarsu a kan hanya sannan suka fara tafiya da kafa zuwa wajen.

 Yayin da ya ke zuwa wurin, ya yi ikirarin cewa an umarce su da cewa su tsaya.

 Anigbo ya ce sun yi biyayya ga sojojin kuma suka tsaya suka fara shaida musu cewa su ’yan banga ne a unguwar.

 “Duk da cewa muna sanye da cikakken kakin jami’an tsaro na 'yan banga, amma sojojin sun bude mana wuta, inda suka kashe marigayi Oke, da matar.

 "Bayan sun harbe ni da yawa, a lokacin da nake a kasa, daya daga cikin sojojin, duk da ganin katin shaida na da kakin 'yan banga da nike sanye da shi, ya sake harbi na a kafada," in ji Anigbo cikin hawaye.

 Amma da aka tuntubi mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 82, Laftanar Kanar Jonah Unuakhalu, ya bayyana wadanda abin ya shafa a matsayin ‘yan bindiga, yana mai cewa labarin nasu ba gaskiya bane.

 Kakakin rundunar ya kuma ce daga bayanan da ake samu a rundunar, an kashe matar ne ta hanyar harsashi da wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka yi.

 Ya ce sojojin sun samu kiran cewa wasu miyagu ne ke gudanar da ayyukansu a kan hanyar Eke inda suka garzaya wurin.

 Da miyagun suka ga sojojin tafe, ya yi zargin cewa ‘yan bindigar sun bude musu wuta amma jami’an sojin sun yi galaba a kansu, lamarin da ya sa aka kama daya daga cikinsu tare da kwato bindigogi masu sarrafa kansu (Action mechine gune) guda biyu da kuma wasu harsasai, yain dawasu suka tsere zuwa cikin daji da ke kusa.

 Kakakin runduna ta 82, ya ce ba shi da wani bayani dangane da mamacin na biyu, inda ya kara da cewa a yayin da ake musayar wuta tsakanin sojojin da ‘yan ta’addan ne harsashin da ya bijirowa matar wadda aka garzaya da ita asibiti.  daga baya ta mutu.

 “Don haka, babu gaskiya a cikin bayanan da ake yadawa cewa sojoji ne suka kashe mariganyar.  Mutanen mu ne kawai suka garzaya wurin domin ceto lamarin, bayan da aka yi masa kiranye.

 "Abin takaici ne cewa matar ta mutu, idan ba haka ba, da ta kasance a matsayi mafi kyau don ba da labarin ainihin abin da ya faru," in ji shi.

 Unuakhalu ya bayyana cewa rundunar za ta gudanar da binciken da ya dace kan lamarin, domin bankado hakikanin abin da ya faru.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN