FG ta kara kudin makarantun Unity daga N45,000 zuwa N100,000


Gwamnatin tarayya ta kara wa sabbin daliban makarantun gwamnatin tarayya kudaden makaranta da aka fi sani da Federal Unity Colleges zuwa ₦100,000. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

 An bayyana wannan karin ne ta wata takardar da aka fitar daga ofishin daraktan sashin kula da manyan makarantun gaba da sakandare na ma’aikatar ilimi ta tarayya, mai kwanan wata 25 ga Mayu, 2023, kuma aka mika ga dukkan shugabannin kwalejojin hadin kan tarayya.

 A cikin takardar da aka yi wa lakabi da, “An amince da biyan kudin shiga makarantun tarayya (Term na farko) ga sabbin dalibai” da kuma daraktan kula da manyan makarantun gaba da sakandire, Hajiya Binta Abdulkadir ta sanya wa hannu, ana sa ran sabbin dalibai za su biya ₦100,000 maimakon Naira 45,000 da ta gabata.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN