Da Ɗumi-Ɗumi: Ɗan Majalisar Tarayya Ya Yi Mummunan Hatsari a Hanyar Koma Wa Abuja


Ɗan majalisar wakilan tarayya kuma tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Marcus Onobun, ya gamu da hatsarin mota ranar Laraba da ta gabata. Legit Hausa ya wallafa.

Hatsarin ya rutsa da ɗan majalisar a Ekpoma-Auchi wani ɓangaren titin Benin zuwa Abuja yayin da yake kan hanyar koma wa Abuja domin halartar zaman majalisa.

Daily Trust ta ce ya kamata Honorabul Onobun ya koma Abuja ta jirgin sama amma rahotanni sun ce ya rasa jirginsa, bisa haka ya yanke shawarar tafiya ta mota.

An tattaro cewa dan majalisar mai wakiltar mazaɓun Esan ta Yamma, Esan ta tsakiya da kuma Igueben a majalisar wakilai ta ƙasa, ya samu rauni a hatsarin.

Bayanai sun nuna motar ɗan majalisar ta yi kaca-kaca a hatsarin wanda suka yi taho mu gama bayan ya bugi wani rami a kan titin.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN