Rahotanni sun kawo cewa Allah ya yi wa matar shahararran dan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Mangal, rasuwa.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Hajiya Aisha Daihuru Mangal ta rasu ne a wani asibitin Abuja a yammacin ranar Asabar, 15 ga watan Yuli bayan ta yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya. Legit ya wallafa.
Wata majiya ta iyalin ta ce za a yi jana'izarta a mahaifar Mangal da ke yankin Kifar Guga, a garin Katsina da misalin karfe 11:00 na safiyar Lahadi, 16 ga watan Yuli.
Marigayiya Hajiya Aisha ta mutu ta bar mijinta, yara da kuma jikoki.
Babban rashi na uku da ya doki dan kasuwar kenan a jere
Wannan shine babban rashi na uku da shahararran ke yi a jere a baya-bayan nan.
A bara ne Allah ya yi wa kaninsa wanda yake shugaban kamfani rasuwa, yayin da dansa ya rasu kafin rasuwar dan uwan nasa, rahoton PM News.
Published by isyaku.com