Wani dan banga mai suna Hamman Joda Isa ya auri wata ‘yar kasar Norway mai suna Diana Maria Lugunborg a garin Yola da ke karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar Adamawa. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
An tattaro cewa Diana ta zo daga Norway kuma ta amince da auren Isa wanda ta hadu da shi a dandalin sada zumunta.
Isah da Diana sun yi aure ne a babban ofishin rajistar babbar kotu da ke garin Yola kwanakin baya.
Bayan haka an gudanar da liyafar daurin aure a wani wurin taron da ke daura da kwalejin koyon shari'a ta Yola.
Published by isyaku.com