Shugaban Kamfanin mai na NNPC, Mele Kyari ya bayyana dalilin tashin farashin mai a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli.
Kyari ya ce wannan tashin farashin ba shi da alaka da karancin man fetur a kasar kamar yadda ake yadawa. Legit ya wallafa.
Ya ce tashin farashin man fetur din na da alaka da sauyin farashi daga 'yan kasuwa, Punch ta tattaro.
NNPP ya bayyana dalilin tashin farashin man fetur
Kyari ya bayyana haka ga 'yan jaridu bayan wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a Abuja, TheCable ta tattaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce karin farashin daga 'yan kasuwa ne kuma ya na iya yin sama ko kasa.
Ya ce:
"Wannan farashi ya danganci 'yan kasuwa ne, wannan shi ne ma'anar 'yan kasuwa su rinka gudanar da farashin.
"Farashin zai na sauyawa, wata rana ya yi sama wata rana kuma ya yi kasa."
Wannan na zuwa ne bayan farashin man fetur ya tashi daga N540 a kan lita zuwa N617 a safiyar yau Talata 18 ga watan Yuli, cewar THISDAY.
Ya karyata rade-radin da ake cewa wai hakan na da nasaba da karancin mai din a kasar.
Ya ce akwai tulin mai a kasar kuma wadatacce
Ya tabbatar da cewa:
"Wannan sauyin farashin ba shi da alaka da yawan mai da ake batarwa, ba wannan ne matsalar ba.
"Idan ka je kasuwa ka sayi kaya, za ka siyar a kasuwa yadda farashin wurin ya kama, babu batun cewa karancin mai ne ya jawo, ba mu da wannar matsalar.
"Muna da wadataccen mai a kasa, mun samar da mai har ma tsawon kwanaki 32, wannan ba matsala ba ne."
A bangarensa, shugaban hukumar NMDPRA, Faroul Ahmed ya alakanta tashin farashin mai din da tsadar danyen mai a duniya.
Ya kara da cewa yawan kashe-kashen kudade yayin shigo da man a bangaren dillalan man fetur shi ma na daga cikin dalilan.
FG Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Mai Bayan Dillalan Man Sun Fara Shigo Da Shi Kasar
Published by isyaku.com