Wani ma’aikacin POS a jihar Adamawa, Umar Faruk Usman ya sha maganin kashe kwari da ake kira Otapiapia, domin ya kashe kansa kan bashin N1.760. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Umar dan karamar hukumar Yola ta Kudu, ya yi yunkurin kashe kansa ne a babbar kotu da ke Yola a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli, 2023, inda abokinsa, Mustapha Baraya, ya kai kararsa kan bashi kudin da ya ba shi.
A cewar wani dan jarida, Jonathan Filibus, abokin nasa mai wannan adireshin ne ya kai karar Umar a ranar 13 ga watan Fabrairu, 2023 saboda "cin amana" sabanin sashe na 299 na dokar penal code 2018 na jihar Adamawa.
Baraya ya baiwa Umar zunzurutun kudi har Naira miliyan 1.960 domin gudanar da sana’ar POS amma Umar ya karkatar da kudaden gaba dayansa, kuma ya mayar da N150,000 kawai cikin kudin.
An tattaro cewa kokarin da mai korafin ya yi na kwato ragowar Naira miliyan 1.760 bai yi nasara ba saboda Umar da mahaifinsa sun ci gaba da yaudararsa duk da hukuncin da kotun ta yanke.
Kotu dai ta umurci Umar da ya mayar da kudin sannan ta ba shi wata guda da zai yi hakan, amma ya kasa mayar da kudin.
Wanda ake kara da mahaifinsa sun sanar da kotun cewa suna da gonar shinkafa da suke shirin girbi, kuma bayan girbi za su mayar da kudaden.
Sai dai abin takaicin shi ne wanda ake kara da mahaifinsa sun je a asirce suka girbe amfanin gona ba tare da sanin kotu ba kuma ba tare da sun mayar da kudin ba.
Kotun dai ba ta da wani zabi da ya wuce ta aiwatar da hukuncin da ta yanke inda ta bayar da umarnin a sayar da gidan Umar da mahaifinsa ya ba shi.
An sayar da gidan kan kudi Naira miliyan 1.1 domin a samu kudin da za a biya mai kara.
Da alamu Usman bai gamsu da matakin da kotun ta dauka ba, ya sayo kwalbar maganin kashe kwari, ya boye a aljihunsa ya kutsa kai cikin kotun da nufin halaka kanshi.
Ya shiga zauren alkali, Hon. Shehu Mustapha, inda ya kwankwade sinadarin fiyafiya ya fasa kwalbar a kokarinsa na kawo karshen rayuwarsa a gaban alkali.
Nan take ya fadi ya fara amai ya sume. Daga baya an garzaya da shi asibitin musamman na Yola domin kula da lafiyarsa cikin gaggawa.
Published by isyaku.com