Da gaske tsaka tana da guba mai kisa? - ISYAKU.COM


A baya-bayan nan dai ana ta yada wani bidiyo a kafafen intanet da ke nuna yadda tsaka ke kashe mutane saboda zargin zuba dafi a abinci ko abin sha.

Shin ko gaske ne wannan labari?

Sashen Hausa na BBC ya miƙa wannan tambaya ga wata ƙwararriyar likitar dabbobi kuma mai kula da asibitin dabbobi da ke Nyanya a Abuja.

Ga kuma fatawar da ta bayar.

"Tsaka ba ta da guba"

Dr Zainab Abubakar ta ce babu wani bincike da ya nuna tsaka na dauke da guba.

"Ba gaskiya ba ne. Tsaka ba ta dauke da guba mai kisa a yawunta ko a jikinta. Ba kamar macizai da ke dauke da guba ba"

To sai dai kuma likitar ta ce tsakar na daukar kwayoyin cuta a jikinta daga ruwa ko kasa.

"Ana samun cutuka daga kashi ko fitasrin tsaka wanda suka dauka a abinci ko abin sha. Ita tsaka tana dauka da yada cutar ne amma ba wai a jikinta yake ba.

Idan akwai illar da za a ce tsaka na da ita, ita ce ce yadda tsakar ke yada cutuka daga fitsari ko kashinta."

Wadanne irin cutuka tsaka ke yadawa?

Tsaka na sanya wa dan'Adam zazzabin Typoid kamar yadda sauran dabbobin gida da na dawa ke yadawa.

"Babu wata dabba da ba ta yada cuta ga dan'Adam. Sai dai kawai wata cutar ta fi wata."

Ta yaya za a yi maganin tsaka a gidaje?

Dr Zainab ta ce abu na farko da ya kamata a yi wajen magance tsaka a gidaje shi ne feshi.

"Shi wannan feshi ya kamata a rinka yin sa a kai-a kai".

Abu na biyu kuma shi ne yin amfani da wasu dabbobin kamar kada ko kadangare ko mage ko kuma karnuka wadanda suke farautar tsakar.

Rahotun BBC

Published by isyaku.com

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. Wannan zancen na Dr Zainab ba gaskiya ba ne, domin Mu Annabinmu Muhammadu SAW ya ce tana da Guba kuma tana kisa.
    Don haka zancenta munyi Allah wadai da shi.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN