Wasu mutane da dama sun tafka sata a wani rumbun ajiyar da aka yi amfani da shi wajen adana buhunan masara da shinkafa da aka sarrafa a cikin gida da dai sauransu a wani dakin ajiyar kaya da ke Jalingo babban birnin jihar Taraba.
Mutanen sun mamaye rumbun ajiyar da ba ta da nisa da 6 Army Brigade, kuma na wani dan majalisar jiha ne kuma tsohon shugaban karamar hukumar Sardauna a daren Juma’a.
Jami’an tsaro da suka isa wurin domin tarwatsa mutanen sun kashe biyu daga cikinsu. Daily trust ta ruwaito cewa kayayyakin da aka kwashe sun hada da daruruwan buhunan masara da shinkafa da aka sarrafa a cikin gida da kuma kayayyakin amfanin gona da suka hada da taki da magungunan kashe kwari.
Hakazalika matasan sun tafka sata a wasu shaguna a yankin. A baya ma, an kai harin sata a gidan ajiyar kayan ajiya a lokacin tarzomar EndSARS na 2020 kuma an yi awon gaba da kayayyaki na miliyoyin naira.
Published by isyaku.com