Wasu ƙananan yara guda biyu, Gbolahan da Olayinka Atolagbe, sun riga mu gidan gaskiya bayan katangar wani gida dake maƙwabtaka da na su ta rufto musu a jihar Legas. Legit ya wallafa.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a lokacin wani ruwan sama mai kama da bakin ƙwarya da aka tafka ranar Asabar, a titin Alao, cikin Isawo a ƙaramar hukumar Ikorodu ta jihar.
An ciro gawarwakin yaran a cikin ɓuraguzan katangar bayan sun kwashe sa'o'i masu yawa yayin da ake ta ƙoƙarin ceto su.
Kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) yankin Kudu maso Yamma, Mr Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Published by isyaku.com