Hajj 2023: Wasu Alhazan Najeriya biyu sun rasu a Saudiyya


Wasu alhazai biyu daga jihar Kaduna sun rasu a yayin da suke gudanar da aikin hajji a kasar Saudiyya.

 Mataimaki na musamman ga babban sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna, Ibrahim Giwa, ya tabbatarwa manema labarai rasuwar a birnin Makkah a ranar Litinin 3 ga watan Yuli.

 Ya bayyana sunayen mahajjatan da suka hada da Bashir Umar Sambo daga karamar hukumar Kubau da kuma Sulaiman Abubakar (Unguwan Lalli) daga karamar hukumar Igabi.

 Alhaji Bashir ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan ya sha fama da jinya a Makkah, kuma tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

 “Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta sanar da rasuwar Sulaiman Abubakar Unguwan Lalli, KD 086 TRK daga karamar hukumar Igabi da Bashir Umar Sambo, KD 318 KB daga karamar hukumar Kubau,” ya bayyana.

 “Wannan ya kawo adadin maniyyatan da suka rasu a Saudiyya zuwa hudu.  Muna rokon Allah ya ba su Aljannah, kuma ya karbe su a matsayin shahidai,” ya kara da cewa.

 Sai dai ya lura cewa an fara shirye-shiryen jigilar alhazai zuwa gida.

 Yayin da yake taya alhazai murnar kammala aikin Hajji cikin nasara, ya shawarce su da su tattalin kudadensu har zuwa ranar dawowarsu ta karshe.

 Daga nan sai ya bayyana cewa an fara rabon manyan kayan alhazai mai nauyin kilogiram 32, ya kuma bukaci wadanda kayansu suka bata dasu je sakatariyar hukumar da ke birnin Makkah don neman kayan.


Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN