Majalisar wakilai a ranar Laraba, 19 ga watan Yuli ta ki amincewa da kudirin dakatar da karin farashin Man Fetur tare da komawa tsohon farashin Naira 537 kan kowace lita.
A maimakon haka majalisar ta amince ta binciki karin farashin mai da aka yi ba zato ba tsammani da kuma karin farashin sufuri a fadin kasar nan.
Majalisar ta ce tunda ta riga ta yanke shawarar yin bincike kan karin farashin man, kuma dakatar da karin farashin man ta hanyar amincewa da kudirin zai kai ga share aikin kwamitin binciken.
A wani kudiri na 'Lamari mai muhimmanci ga jama'a cikin gaggawa' da Hon. Ikenga Ugochinyere ya gabatar, Majalisar ta bukaci kungiyar Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Nigeria National Petroleum Company Limited, Mele Kyari da ’yan kasuwar mai da su gurfana a gaban kwamitin wucin gadi don bayyana dalilin karin kudin.
Published by isyaku.com