Gwamnan jihar, Dr. Nasir Idris, (Kauran Gwandu) ya ayyana ranar Laraba 19 ga watan Yuli, 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, Muharram 1445H.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Safiyanu Garba Bena wanda aka rabawa manema labarai ranar Talata a Birnin kebbi.
Sanarwar ta ce, hakan ya biyo bayan ayyana ranar Laraba 19 ga watan Yuli a matsayin 1 ga watan Muharram, wata na farko na sabuwar shekara ta Musulunci ne domin baiwa al'ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan sabuwar shekarar Musulunci.
Published by isyaku.com