A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ganawarsa ta farko da sabbin shugabannin ma’aikatun tsaro da aka nada kwanan nan.
An gudanar da taron ne a fadar gwamnatin taraya dake Abuja. Jaridar PM News ta rahoto.
Babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ne ya jagoranci shugabannin hukumomin zuwa dakin taron.
A wajen taron akwai Manjo Janar Christopher G Musa, babban hafsan hafsoshin tsaro;
Manjo Janar, A Lagbaja, babban hafsan sojin kasa; Rear Admiral Emmanuel A Ogalla, babban hafsan sojin ruwa; Air Vice Marshal Hassan B. Abubakar, Hafsan Hafsoshin Sojan Sama; Mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun da Manjo Janar Emmanuel P.A. Undiandeye, shugaban hukumar leken asiri na tsaro.
Tinubu dai ya tafi kasar Faransa ne a daidai lokacin da ya nada sabbin shugabannin ma’aikatun kuma ya dawo Abuja ranar Lahadi.
A ranar 19 ga watan Yuni, 2023 shugaban ya kori tsoffin hafsoshin tsaro tare da nada sababbi.
Published by isyaku.com