An cafke saurayi da ya kwada wa dan acaba karfe a kai ya gudu da babur


Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta cafke wani da ake zargin dan fashi da makami ne da ya kai wa wani dan kasuwa hari da wani karfe kafin ya kwace babur dinsa a karamar hukumar Jama’are ta jihar.

 Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 14 ga watan Yuli, 2023, ya ce wanda ake zargin, Munkailu Haruna, sun fito ne a matsayin fasinjoji suka hau babur din wanda abin ya shafa.

 “A ranar 14/07/2023 da misalin karfe 0700 na safe wani mutum mai suna Saleh Ahmadu ‘m’ na kauyen Ayas Jama’are karamar hukumar Jama’are wani direban babur ya ba da rahoton cewa a ranar 13/07/2023 da misalin karfe 2030, wasu mutane biyu da ba a san ko su wanene ba suka hau babur dinsa mara rajista daga garin Jama’are zuwa kwalejin Jama’are da ke wajen garin Jama’are,” in ji sanarwar.

 “Da isar su makarantar ne suka yi amfani da wani karfe suka buga masa kai, suka kwace babur dinsa, sai ya daga kararrawa mutane suka kawo masa dauki, ana cikin haka sai wadanda ake zargin suka bar babur din suka tsere.

 “Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO ta koma wurin da lamarin ya faru.  An kama wani Munkailu Haruna ‘m’ mai shekaru 22 a kauyen Gandiyel karamar hukumar Itas Gadau.”

 An sami wuka daya, sandar karfe daya da aka yi amfani da su wajen aikata wannan danyen aiki da kuma buhu daga hannun wanda ake zargin.

 PPRO ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN