Labari Mai Zafi: Kotun Zabe Ta Yi Hukunci Kan Karar Zaben Gwamnan Jihar Adamawa


Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Adamawa, ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar Action Alliance (AA) ta shigar inda ta ke ƙalubalantar nasarar gwamna Ahmadu Fintiri.

Jam'iyyar ta AA dai tana ƙalubalantar bayyana gwamnan jihar Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar a ranar 16 ga watan Afirilun 2023, cewar rahoton Channels tv.

Jam'iyyar wacce ta shigar da ƙarar ta janye ƙarar a hukumance wanda hakan ya sanya kotun ta yi fatali da ƙarar a zamanta na ranar Juma'a a birnin Yola, babban birnin jihar Adamawa, rahoton Sahel Reporters ya tabbatar. 

Jam'iyyu uku na ƙalubalantar nasarar Ahmadu Fintiri a gaban Kotu

Ƙararraki uku aka shigar kan bayyana Fintiri da jam'iyyar PDP a matsayin waɗanda suka yi nasara a zaɓen ta hannun jam'iyyar AA da ɗan takararta, jam'iyyar SDP da ɗan takararta Dr. Umar Ado da jam'iyyar APC da ƴar takararta Sanata Aisha Dahiru Binani.

Binani na neman kotu da ta tabbatar da bayyanata a matsayin wacce ta lashe zaɓen da Hudu Yunusa Ari ya yi.

Kotu ta yi watsi da ƙarar jam'iyyar Action Alliance bayan mai shigar da ƙarar da lauyoyinsu sun sanar da kotun sun janye ƙarar.

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ɗan takararta Fintiri sun shigar da kuɗiri a gaban kotun na ta yi watsi da ƙarar da jam'iyyar APC da ƴar takararta suka shigar.

A ɓangaren jam'iyyar SDP, lauyan jam'iyyar ya kasa kawo hujjoji a gaban kotun. An ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 21 ga watan Yulin 2023.

Binani Ta Sake Kai INEC Kara a Gaban Kotu
A wani labarin kuma, ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC ta sake kai hukumar INEC ƙara a gaban kotu.

Aisha Dahiru Binani ta kai ƙarar hukumar zaɓen a gaban kotu ne saboda soke sanar da ita a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan jihar.

Legit

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN