Wani jirgin yakin sojojin saman Najeriya a ranar Juma'a, 14 ga watan Yuli, ya yi hatsari a Makurdi, babban birnin jihar Benue.
Har yanzu dai ba a san abin da ya haddasa hatsarin ba, sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu jami'an rundunar sojojin saman Najeriya biyu da ke cikin jirgin sun koru ba tare da jin komi ba. Wata majiya ta shaida wa jaridar;
“Jirgin FT7-NI ya yi hatsari a yau a Makurdi. Har yanzu dai ba a iya gano musabbabin hatsarin jirgin ba. Akwai Airmen guda biyu a cikin jirgin. Sun fita ba tare da jin rauni ba daga jet."
Published by isyaku.com