Mutane 11 daga Bauchi sun rasu a hatsarin mota a jihar Kaduna, yadda ta faru

Daga Muazu Hardawa Bauchi


Ranar juma'a da ta gabata ne aka Yi janazar mutane 11 da hatsarin Mota ya rutsa da su a kan hanyar su ta zuwa  Onisha domin kai dabbobi da kuma wasu masu niyyar tafiya kudanci domin neman kudi daga karamar hukumar Darazo.

Hatsarin ya abku a wani sashe na Jihar Kaduna inda mutanen Lanzai guda takwas suka rasu. Yayin da mutum biyu daga  Sade da kuma mutum guda daga Dambam suka rasu.

Malam Ibrahim Hamza majikiran Lanzai na cikin wanda ya rasa yan uwansa a hatsarin kuma na zanta da shi, inda ya ce an yi hatsarin a daren ranar alhamis, kuma an kwaso mamatan dukkan su zuwa gida an yi janazar su ranar juma'a da ta wuce a garuruwa su.

Ya kara da cewa tsadar kudin Mota ya sa mutane Yan kasuwa da Yan ci rani suke hawa manyan motocin kaya don yin tafiya, yadda idan aka samu hatsari ake rasa rayuka masu yawa.

Saboda mutanen da abin ya shafa suna da yawa, Amma wannan adadi na yankin Darazo da Dambam ne, yayin da wasu kuma.da dama sun samu raunuka an kai su asibiti.

Dukkan kokarin da muka yi don jin ta bakin hukumomin Yan sanda da na hukumar kiyaye hadurra daga Jihar Kaduna lamarin ya ci tura.

Daga Muazu Hardawa Bauchi.

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN