Wasu da ake kyautata zaton barayin babur ne sun sha dan karen duka a hannun fusatattun mutane a karamar hukumar Agaie ta jihar Neja.
Ana zargin cewa wadanda aka kama sun dade suna addabar jama’ar garin, inda suka yi awon gaba da babura tare da wasu kayayyaki masu daraja.
A cewar mazauna garin, wadanda ake zargin sun kwace banur na wani dan acaba bayan sun kashe shi.
Sai dai kuma, sun yi rashin sa’a bayan an kama su yayin wani samame da ake zargin sun kai a unguwar G.R.A da ke garin a daren Alhamis 1 ga watan Yuni, 2023.
‘Fusatattun Mutane sun cafke wadanda ake zargin suka lakada musu duka.
BY isyaku.com