An sanar da rushe kungiyar Yan kasuwar Kebbi Market Traders Association KEMTA ranar Juma'a 2 ga watan Yuni 2023. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Mai magana da yawun kungiyar, PRO Kasimu A. Bawa ya sanar da haka ga manema labarai a garin Birnin kebbi.
Kasimu ya ce Gwamnatin jihar Kebbi ta hannun Ahmed Yarima, Sakataren dindindin na ma'aikatar Kasuwanci (Ministry of Commerce) ta amince da rushe shugabacin kungiyar, kuma ta amince da kafa kwamitin rikon kwarya da suka hada da:
1. Alhaji Mustapha Speaker - Chairman
2. Sidi Zanna - Secretary
3. Kasimu A. Bawa - PRO
4. Alhaji Yunusa Mai Atamfa - Treasurer
BY isyaku.com