Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada Sanata George Akume, tsohon ministan ayyuka na musamman a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar Abiodun Oladunjoye ya fitar ranar Juma’a. Daily trust ta rahoto.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Juma’a a Abuja ya sanar da nadin kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikata, da Sen. Ibrahim Hassan Hadejia, tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa a matsayin mataimakin shugaban ma’aikata.
“A ganawar da shugaban ya yi da Progressive Governors Forum (PGF), shugaban ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman, George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF).”
BY isyaku.com