Wasu mazauna jihar Edo sun toshe babbar hanyar Benin zuwa Legas da wasu yankuna a cikin birnin Benin sakamakon karin farashin farashin man fetur.
Masu zanga-zangar wadanda akasari mambobin kungiyar farar hula ne ta Jihar Edo (EDOCSO), sun yi kira da a gaggauta sauya farashin famfon man. Daily trust ta rahoto.
Rike alluna masu rubuce-rubuce irin su "'Yan Najeriya ba za su iya siyan fetur a kan Naira 520 ba"; "Ba za mu iya sayen man fetur a kan Naira 520 ba sai N210"; "Dole ne man fetur ya kasance N210 har zuwa karshen Yuli", masu zanga-zangar sun ce 'yan Najeriya sun riga sun fuskanci kalubale da dama.
Hakan ya tilasta wa masu ababen hawa yin tattaki zuwa inda za su je.
Da yake jawabi ga manema labarai, tsohon kodineta Janar na Edocso, Omobude Agho, ya ce sun yi zanga-zangar ne domin a jawo hankalin shugaban kasa Bola Tinubu domin ya duba farashin man fetur.
“Muna zanga-zangar ne saboda karin farashin man fetur da aka fara a jiya, ‘yan kasuwa sun canja farashin daga N210 zuwa sama da N500.
“Mun yi mamakin ganin hatta Kamfanin NNPC Limited ya kayyade sama da Naira 500 a matsayin farashin famfo. Don haka muna jin wannan shiri ne na kashe ’yan Najeriya ko kuma a kai mu kabarinmu.
“ A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da shi a wurare irin su Uselu shell, Ologbo, Siluko da Agbor park.”
Ya kara da cewa idan har zuwa ranar Juma'a gwamnati ta kasa shawo kan lamarin, zanga-zangar za ta yadu zuwa wasu yankuna.
BY isyaku.com