Manyan Yan Najeriya Na Gaba Da Tinubu Zai Yaka Idan Ya Yi Nasarar Cire Tallafin Mai Da Dalili


Shugaban kasa Bola Tinubu ya tsaya tsayin daka kan maganarsa na cika aiki tun daga jawabinsa na farko bayan rantsar da shi kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabensa. Legit ya wallafa.

Gwamnatocin baya sun sha yin magana kan barazana da hatsarin tallafin mai ga tattalin arzikin Najeriya amma sun gaza cire shi yayin da yan kasuwa ke saurin kara farashin man fetur da kuma sawa ya yi karanci a kasuwa, wanda galibi yake sa yan kasa yin zanga-zanga.

Sai dai kuma, da alama gwamnatin Tinubu ta daura damarar cire tallafin man fetur din da tabbatar da ganin cewa bai sake bayyana a tattalin arzikin Najeriya ba da yanayin yadda take gudanar da harkokinta.

Saboda haka, idan Tinubu ya yi nasara a yakinsa da tallafin mai, abu na gaba da sabuwar gwamnatin za ta iya sanyawa a gaba ita ce 'Kasuwar chanji', wani tsari da yan tsirarun mutane ke amfana da shi da kuma yin illa ga farashin chanjin kudin kasar.

Harkar canji yana kunshe da manyan yan Najeriya wadanda ke siyar da dala a 'kasuwar bayan fage'.

Wadannan mutane na samun dala masu yawan gaske daga babban bankin Najeriya (CBN), ta hanyar amfani da sanayya da kamun kafa sannan su sake siyar da su da tsada a kasuwar bayan fage.

A ranar Laraba, 31 ga watan Mayu, farashin chanji a hukumance ya kasance N461 kan kowace dala yayin ake siyar da shi kan N745 a kasuwar bayan fage.

Dalilin da zai sa Tinubu ya yaki yan chanji

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati a ranar Talata, 30 ga watan Mayu, wacce ta kasance ranarsa ta farko a ofis, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa sun nuna turjiya sosai a kan sabuwar manufar amma sabuwar gwamnatin tana da niyan karya shi.

A cewar Shettima, dole tallafin man fetur ya tafi sannan dole ninkanya a farashin chanji ya tsaya. Ya kara da cewar idan Najeriya bata kawo karshen tallafin ba, tallafin zai kawo karshen Najeriya.

Shin Tinubu zai yaki tallafi da yan chanji?

Lokaci ne zai nuna ko Tinubu zai yi nasara a yaki da ya daukarwa kansa da gwamnatinsa.

Hakan ya kasance ne saboda tsarin chanjin kudin kasar ya dade kamar dai tallafin, idan ma bai fi shi tsufa ba, kuma ya zama ruwan dare da yaki da shi zai zama kamar raba wasu mutane da hanyar cin abincinsu a kasar

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN