Yanzu-Yanzu: "Zan Iya Marin Kwankwaso Da Mun Hadu a Villa" Ganduje Ya Fusata da Abinda Ke Faruwa a Kano


Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa idan da ya hadu da magajinsa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, a fadar shugaban kasa da ke Abuja da ya mare shi.

Mun dai ji cewa Kwankwaso ya gana da shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa a ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, rahoton Daily Trust.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu kan lamarin tsaro a jihar Kano bayan aikin rusau da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Ganduje ya nuna rashin gamsuwa da lamarin. Legit ya wallafa.

"Na san yana gidan amma ba mu hadu ba. Amma da ace mun hadu, watakila da na mare shi."

Ana ta rusau a Kano ba bisa ka'ida ba, Ganduje

Ganduje ya ce an gudanar da shirin rusau din ba tare da kowani bincike ko bayar da sanarwa daidai da dokar fili ba.

Tsohon gwamnan ya ce ya yi magana sosai kan lamarin yayin da yake kaiwa shugaban kasar rahoton lamarin kuma cewa ya aikewa Sufeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba bayani kan lamarin da bidiyon sace-sacen da ya biyo bayan rusan.

Ya ce gwamnan wanda ya bayyana shi a matsayin karen farautar Kwankwaso baya jin dadi a yanzu saboda sukar da ya biyo bayan lamarin.

Tinubu ya gana da Kwankwaso a fadar Villa
Mun kawo a baya cewa shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso a Aso Rock, Abuja.

Kwankwaso na ɗaya daga cikin manyan 'yan takarar shugaban ƙasa na sahun gaba da suka kara da Tinubu a zaben 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN