Yanzu yanzu: Yan sanda sun kai samame gidan tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle sun kwace motoci

Bello Matawalle motoci da Yan sanda suka kwace a gidansa

An kwace wasu motoci daga gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle da ke Gusau babban birnin jihar. Daily trust ta rahoto.

 Majiyoyi sun shaida wa Daily trust cewa an kwace Motoci (SUVs) ne a wani samame da aka kai gidan Matawalle na GRA da ke Gusau, a ranar Juma’a.

 Daily trust ba za ta iya tabbatar da adadin motocin da aka gano ba, amma wata majiya ta ce an kwace jimillan motocin jeep guda hudu.

 An ce ‘yan sanda sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan, wanda ba shi da nisa da gidan gwamnati, Gusau.

 Daily trust ta kasa samun Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazdi Abubakar, saboda wayarsa ta yi ta Kara har ta yanke bai dauka ba yayin da jarida ta yi kokarin jin ta bakinsa kan lamarin.

 Har ila yau, mai ba tsohon gwamna shawara a kan wayar da kan jama’a, harkokin yada labarai da sadarwa, Zailani Bappa, shi ma ba a same shi ba har zuwa lokacin da wannan rahoto ya fito domin a kashe layukan wayarsa.

 Kwanaki biyu da karbar ragamar mulki, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya zargi Matawalle da ficewa da motocin gwamnati 17 tare da wawashe kadarori da suka hada da talabijin da na'urorin dafa abinci a gidan gwamnatin jihar.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN