Ta faru ta kare: 'Yan sanda sun kwamushe kasurgumin barawon shanun da ya addabi mutane

Sale Kabo kasurgumin barawon shanu a Gombe isyaku.com

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wani matashi da ake zargi da satar shanu har na N7m a jihar.

Wanda ake zargin mai suna Sale Kabo dan shekara 30 ya fito ne daga kauyen Bandila a karamar hukumar Gulani ta jihar Yobe. Legit ya wallafa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Abubakar ne ya bayyana haka inda yace Kabo ya sace shanun ne a karamar hukumar Funakaye da ke cikin jihar Gombe, cewar Tribune.

Wani dattijo a kauyen ne ya kawo rahoton ga rundunar 'yan sanda
Ya bayyana cewa Jauro Ahmadu mai shekaru 75 na kauyen Shuwari a cikin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye ne ya kawo rahoton hedkwatar ‘yan sanda na yanki da ke Bajoga.

Mahid ya ce Ahmadu ya tabbatar da cewa an sace masa shanu 21 da kudinsu ya kai N7m a kauyen da tsakiyar dare, cewar Punch.

Tuni rundunar 'yan sandan ta umarci da a fara bincike kan satar shanun

Kakakin ya kara da cewa, rundunar ta umarci da a fara gabatar da bincike don sanin tushen lamarin da kuma dakile sace-sacen shanu a jihar gaba daya nan gaba.

A cewarsa:

“Bayan bincike mai zurfi, an yi nasarar kama Sale Kabo dumu-dumu a satar shanun wanda ya tabbatar da cewa shi ya sace su, yayin da dukkan shanun da ake zargin an sace aka same su a hannunsa da sauran abubuwan da ke da alaka da satar.

“Wanda ake zargin yanzu haka ya na hannun jami’an ‘yan sanda kuma za a tasa keyarsa zuwa kotu da zarar bincike ya kammala."

Maharan sun kai harin ne a safiyar Laraba 7 ga watan Yuni a Kauyen inda suka yi gumurzu kafin sace yaran.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN