Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Mayar Da Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Arewa Da Aka Tsige Kan Mukaminsa


Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a birnin tarayya Abuja, ta mayar da Mahadi Aliyu Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa Gusau da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun shigar da ƙara ne kan hanyar da majalisar dokokin jihar ta bi ta tsige shi daga muƙaminsa a watan Fabrairun 2022. Legit ya wallafa.

Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Laraba, mai sharia Inyang Ekwo ya bayyana cewa kwamitin bincike da tsohon gwamnan jihar Bello Matawalle ya kafa ya saɓa doka, cewar rahoton The Cable.

Kotun ta bayar da umarnin a mayar da shi kan muƙaminsa

Alƙalin ya bayar da umarnin mayar da Mahadi muƙamin mataimakin gwamna tun daga ranar da ya shigar da ƙara a watan Yulin 2021.

Ya kuma kawar da dukkanin matakai da hanyoyin da aka bi wajen tsige mataimakin gwamnan a lokacin da ƙarar ta ke a gaban kotun.

"A dalilin hakan an bayar da umarnin mayar da wanda ya shigar da ƙara (Mahadi Aliyu Mohammed) kan muƙaminsa na mataimakin gwamnan jihar Zamfara, tun daga ranar 8 ga watan Yulin 2021 lokacin da aka fara sauraron wannan ƙarar."

 A cewar alƙalin.

"An kuma bayar da umarnin jingine duk wani hukunci da waɗanda ake ƙarar suka ɗauka wajen tsige mataimakin gwamnan jihar Zamfara, a lokacin da wannan ƙarar ta ke a gaban kotun nan.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

1 Comments

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

  1. KUWA BAYAN YAKI TUNDA GWAMNATI YA KARE SAI A MAYAR DA SHI A OFISHIN SABON MATAIMAKIN GWAMNA KENAN? WANI IRIN HUKUNCIN KOTU SAI NAJERIYA WALLAHI

    ReplyDelete
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN