A ranar Larabar da ta gabata ne tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya mika ragamar jagorancin rundunar ‘yan sandan Nijeriya ga mukaddashin IGP Kayode Egbetokun.
An yi bikin mika kayayyakin ne a hedikwatar rundunar da ke Louis Edet House, Abuja. Shafin isyaku.com ya samo.
Da yake magana, Usman Baba ya ce ya bar rundunar ‘yan sandan Najeriya fiye da yadda ya tarar da ita, ya kuma kara da cewa aikin ‘yan sanda ya kara daraja a Najeriya.
“Yayin da na fice daga shugabancin rundunar a yau, na yi imanin cewa na bar ta fiye da yadda na same ta. Na yi imanin cewa na kara darajar aikin 'yan sanda a Najeriya".
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com